An yi kamen a ciki da wajen gundumomin birnin Brussels, da binciken kowacce gida a kokarin da suke yi na gano wadanda ake zargi da hannu a kai harin.
Sai dai 'yan sanda ba su bayyana sunayen wadanda suke tsare da su ba, a bangare guda kuma jami'an tsaro sun gano wasu mutane biyu da ake zargin sun gudu bayan kai harin.
An dai gano su ne a hotunan internet tare da wanda ake zargi a filin jirgin sama da tashar jirgin kasa wuraren da bama-baman suka ta shi.288